An rufe makarantun kwana 30 a jihar Adamawan Najeriya

An rufe makarantun kwana 30 a jihar Adamawan Najeriya

Sakamakon matsalolin tsaro an rufe makarantun kwana 30 a jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya.

Kwamishinan Ilimi da Gina Dan Adam na jihar Adama Wilbina Jackson ya fitar da rubutacciyar sanarwar cewa, yadda ake yawan kai hare-hare kan makarantu a jihar na da ban tsoro.

Jackson ya kuma shaiwa cewa, gwamnan jihar Adamawa Ahmad Fintiri ya bayar da umarnin a rufe makarantun jihar har nan da lokacin da za su sake bayar da wani umarni.

Ya ce, makarantu 4 da ba na kwana ba a jihar ne za su ci gaba da kasancewa a bude zuwa wani lokaci.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)