'Yan tawaye sun kashe fararen hula 30 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

'Yan tawaye sun kashe fararen hula 30 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Fararen hula 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawaye suka kai a Bunia Babban Birnin jihar Ituri da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, 'yan tawayen Dakarun Hadin Kan Demokradiyya ne suka kai hari a yankin Mapasana na garin Bunia inda suka kashe fararen hula 30.

Mazauna yankin sun shaida cewa, an harbi mutanen da bindiga tare da kashe su, kuma an gano jikkunansu a dazukan Tsani Tsani da ke Mapasana.

An bayyana cewar, 'yan tawayen sun kashe fararen hular a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)