Cutar sankarau ta yi ajalin mutane 129 a Kongo

Cutar sankarau ta yi ajalin mutane 129 a Kongo

Cutar sankarau ta yi ajalin mutane 129 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Wakiliyar Hukumar Lafiya ta Duniya a Kongo Dr. Amedee Prosper Djiguimde ta shaida cewa cutar ta kama mutane 267 a kasar.

Djiguimde ta kara da cewa, tun aga watan Yuni zuwa yau cutar sankarau ta yi ajalin mitane 129 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Ta ce, ana kula da wasu masu dauke da cutar a gidajensu, wasun su kuma a asibitoci, suna kuma ci gaba da sanya idanu kan sake kamuwa da cutar.

 

News Source:  TRT (trt.net.tr)