An fara caccakar hukumar tace fina-finai kan Adam Zango

An fara caccakar hukumar tace fina-finai kan Adam Zango
Hakkin mallakar hotoFALALU DORAYI FACEBOOK

Matakin da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce za ta dauka a kan Zango, ya sa wasu daga cikin 'yan fim ba su ji dadi ba, Falalu Dorayi kuma na daga cikinsu.

Falalu Dorayi, mai shirya fim da bayar da umarni ne, sannan kuma ya kan fito a matsayin jarumi a wasu lokutan a cikin fina-finan hausa na Kannywood.

Falalu na daga cikin makusantan Adam Zango a Kannywood.

Ya kuma wallafa a cikin shafinsa na Instagram cewa:" Idan har hukuma za ta ba wa film satifiket a nuna shi a cinema, duk da akwai jarumai marasa rijista da hukumar a shirin, babu hujjar hana jaruman cikin film din zuwa su gana da magoya bayansu.

"Idan akwai hujjar, za ta fara ne daga lokacin da film din ya zo hannun hukumar, sai su hana satifiket su ce wane ba shi da rijista da mu".

Falalu ya ci gaba da cewa, "abin da mamaki, na san jarumai da mawaka da dama da ba su da lasisin hukumar suna halartar wurin nuna fim a Filmhouse, wani fim din su ne a ciki, wani kuma kallo kawai suka je.

"Ba a taba yunkurin kama su ba, sai rana tsaka a ce an hana wani saboda ba shi da lasisin hukuma".

Wannan layi ne

Daraktan fina-finan ya ce "Adalci shi ne a yi hukunci na bai daya babu nuna fifiko, mene ne bambancin sa da Dija?

"Ba a kano take ba, ba a Kano yake ba, idan har za a bar ta ta zo me zai hana Zango zuwa?

"Ba na jin Dija na da lasisin hukumar, haka kuma idan za a bar wadancan jarumai da mawaka marasa lasisin hukuma su zo kallo, me yasa aka hana Zango?," a cewar jarumin.

Kungiya ra'ayi ce, idan kaga abin da kungiya take baya gamsar da kai, kana da ikon fita, kuma ba a kan Zango aka fara fita daga kungiya ba, Adam A. Zango ya sanar ya fita daga kungiya, amma ba shi ne yake nuna ya daina zamunci da Kano ba.

"Me yasa hukuma take kokarin mayar da abin ya zama hada husuma? Ni dai ban taba ji Zango ya zagi ko cin zarafin Kano ba, kar mu yi amfani da siyasa mu jefi 'yan uwanmu da sharri."

ZangoHakkin mallakar hotoZango

Jagora nagari ana so niyyarsa ta zamo mai kyau ba ta son zuciya ba, sannan ya zamo mai yin abu domin Allah ba domin a gani a fada ba, kuma kar ya zamo mai aibata ko cin zarafin mutane, in ji Falalu Dorayi.

"Idan jagora yana so wadanda yake jagoranta su yi masa biyayya, sai ya yi jagoranci da adalci, ya kiyaye nuna fifiko, ya bai wa dokar gaskiya dama ta yi aiki, ba dokar fadi a baki ba," Falalu Dorayi ya fada.

Falalu Dorayi ya ce " Jagora ya zamo mai aiki da mashawarta nagari, kar ya zamo mai mulki domin bukatar wasu, hakan shi ke kawo mulkin zalunci, har ta kai ana kin girmama juna".

Daga karshen martanin daraktan fina-finan, ya kawo tunatarwa a cikin ayoyin al-Qur'ani mai girma kamar haka:

Qurani a cikin An-Nisa'i (58)

Allahu (SWT) Ya ce:"Lallai ne Allah yana umarnin ku bayar da amanoni zuwa ga masu su."

Wannan layi ne

Matashiya

Falalu Dorayi ya mayar da wannan da martani ne bayan da hukumar ta ce fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta ce dole tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim.

Adam A. Zango dai ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'.

Sai dai jim kadan bayan hakan ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma'ila Na'abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar.

Isma'ila Na'abba Afakallah ya ce Zango yana cikin wadanda ba su yarda sun yi rijista da hukumar ba hasali ma ya ce ya fita daga tsare-tsaren hukumar.

A watan Agustan 2019 ne Adam A. Zango ya ce ya fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Tauraron fim din kuma mawaki ya ce daga yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sai dai bai yi karin haske ba game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood.

Amma ya yi zargin cewa "ana yin shugabancin kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki saboda kwadayi da son zuciya.

News Source:  www.bbc.com