Hotunan abubuwan da suka faru a Kannywood a wannan makon

Hotunan abubuwan da suka faru a Kannywood a wannan makon
Hakkin mallakar hotoIntagram/realabmaishadda
Image caption Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya samu karuwa ta haihuwa. Matarsa ta haifi zankadediyar budurwa wadda ya wallafa hotonta a shafinsa a ranar Asabar. 'Yan uwa da masoya da abokan sana'a na ta addu'o'in taya murna
Yakubu Usman MpegHakkin mallakar hoto@realalinuhu
Image caption Editan Kannywood Yakubu Usman Mpeg, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu. Jaruman masana'anta da masoyansa sun yi ta aika masa sakonnin taya murna
Baban Chinedu da AfakallahHakkin mallakar hoto@officialkannywood
Image caption Dambarwa ta kunno kai bayan Yusuf Haruna (Baban Chinedu) ya zargi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma'il Na'Abba Afakallahu, da karkatar da naira miliyan biyar da gwamantin jihar Kano ta bayar a matsayin gudummuwa a lokacin bikin diyar marigayi Rabilu Musa Ibro
Nura M InuwaHakkin mallakar hoto@nura_m_inuwa
Image caption Ko dai an yi wa Nura M Inuwa nadin sarauta ne? A wace masarauta, kuma wace saurauta aka ba sh? Irin wannan nadi haka!
Adam A. Zango tare da Isma'il Afakallah a lokacin da suke dasawaHakkin mallakar hoto@officialkannywood
Image caption Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce dole tauraron Kannywood Adam Zango ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim. Hakan na zuwa ne bayan bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa na Zango yana cewa zai je Kano domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'.
Ali NamenjHakkin mallakar hoto@namenj
Image caption Namenj ya fitar fitar da hotonsa a lokacin daukar wata waka da ya yi cikin harshen turanci.
Mustapha NabraskaHakkin mallakar hoto@mustapha_nabraska
Image caption Allah Ya raya 'yan mata, Ya kara wa mai jego lafiya! Jarumi Mustapha Nabraska ya samu karuwar 'ya mace a ranar Asabar 22 Fabrairu, 2020.
.
Image caption Tauraruwar Kannywood, Aisha Dankano ta cika shekaru hudu da rasuwa. Allah Ya garfarta mata, mu ma idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe
News Source:  www.bbc.com