Me ya bambanta birnin Lagos da sauran biranen Afirka?

Me ya bambanta birnin Lagos da sauran biranen Afirka?

An fara wallafa shi ranar 15 Nuwamban 2019.

Maraba da zuwa birnin Lagos; birnin da ake hada-hada a ko da yaushe, cike da ya ke mafarkai, da burin su tabbata, inda babu abin da yake gagara matukar ka tsallake siradin cunkoson ababen hawa da ya yi kaurin suna a kai.

Hakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Mutum-mutumin Idejo shi ake fara gani lokacin da aka shiga birnin Lagos

Wakilin BBC Nduka Orjinmo ya ce sarautun gargajiya na da matukar muhimmanci a Najeriya, kuma shi ne nuna karfin ikon wadanda ake damawa da su a kasar.

Babban abin da ya yi wa birnin Lagos cikas shi ne cunkoso, da zarar ka bar filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin, za ka ji yanayin ya sauya tamkar iska ba ta kadawa idan aka kwatanta da sauran biranen Najeriya.

'Kowa na neman na kai'

Duk da cewa birnin Abuja ya maye gurbin Lagos a matsayin babban birnin Najeriya a shekarar 1991, an yi ittifakin ya na daya daga cikin birane masu muhimmanci a kasar, wajen gwagwarmaya da neman na kai a wani bangaren cibiyar kasuwancin kasar.

Aerial view of Jankara market and business area in Lagos IslandHakkin mallakar hotoGetty Images

'Yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar, kama daga ma'aikata da 'yan kasuwa, da 'yan boko, masu mukamai daban-daban na kwarara birnin Lagos cibiyar kasuwanci da nufin samun tagomashin da ke makare a cikinsa.

Lagos na cike da tsofaffi da sabbin masana'antu, da bankuna da kamfanonin fasaha da sauransu. Sannan wuri ne da manyan tashoshin jiragen ruwa biyu su ke, da fitattun kasuwanni masu da daddun tarihi da ke saida kusan duk abin da dan adam zai yi tunani kama daga tufafi, littafai, zane-zane, kayan laturoni da sauransu.

Kantin saida littafai a birnin LagosHakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Kantin sayar da littafai a birnin Lagos

"Akwai damar ayyuka daban-daban a Lagos, wanda da wuya ka samu irinsu a wani yanki a kasar nan," inji Funmi Oyatogun, shugaban kamfanin TVP mai shirya tafiye-tafiye.

Ya kara da cewa ''A lagos kowa ka gani ya na kokarin neman na kai, da magance wata matsala da ka iya tasowa, kirkirar wani sabon abu da za a amfana da shi, kowa cikin hada-hada ya ke a birnin nan.''

'Gwagwarmaya da neman na kai'

Iskar da ke kadawa a birnin Lagos ta daban ce, a dumame ta ke cike da hayaniya da burarin ababen hawa kama daga babur, da motoci manya da kanana, karar injinan janareto, ya yin da miliyoyin mutane na zuruftu a tituna da motocin bs-bas ruwan dorawa da yaran mota da ke kwada kiran unguwannin da motocinsu za su je, a takaice komai a gaggauce ake yi a birnin.

Yadda cunkoson ababen hawa ya cika kasuwar Oshodi da ke LagosHakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Yadda cunkoson ababen hawa ya cika kasuwar Oshodi da ke Lagos

Wani kiyasi da aka yi ya nuna adadin mutanen birnin zai karu zuwa miliyan 88 daga nan zuwa shekarar 2100, hakan na nufin birnin na cike da kalubale musamman yadda ba shi da wadatattun ababen more rayuwa, sai dai duk da hakan mutanen Lagos jajirtattu ne za su iya shanye duk wata wahala.

"Mutanen Lagos sun banbanta da na sauran biranen Najeriya," inji Chimamaka Obuekwe, shugaban kamfanin shirya tafiye-tafiye na Social Prefect Tours. "Mutane ne masu jajircewa dan cimma burin abin da suka sanya a gaba, masu haba-haba da mutane da barkwanci.''

Wani mutum na sayan balangu da aka fi kira suya a LagosHakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Wani mutum na sayan balangu da aka fi kira suya a Lagos

Lagos birni ne da ragwaye ba za su iya zama ba, ya na bukatar kazar-kazar da zafin nama a duk abin da za ka sanya gaba. Matukar ka na son cimma nasara kan abin da ka sanya gaba, dole ka ajiye kasala gefe guda dan tunkarar abin sannan Lagos wuri ne da ke sauyawa mutum tunani musamman ta fuskar dogaro da kai.

'Cibiyar al'adu'

Akwai wasu abubuwa daban masu kayatarwa a Lagos baya ga kasuwanci, shekaru da dama an amince Lagos na daga cikin birane masu tarin al'adu, hakan ya sanya har kawo yau ake damawa da su a wannan fage musamman a masana'antun fina-finan da kade-kade da raye-raye da kuma uwa uba kaya kayan kawa ko kwalliya.

Model Aduke Shitta-Bey kenan a lokacin makon kayan kawa da aka yi a shekarar 2018

Mai tallan kayan kawa kenan Aduke Shitta-Bey kenan a lokacin bikin makon da a ka yi a shekarar 2018
Image caption Mai tallan kayan kawa kenan Aduke Shitta-Bey kenan a lokacin bikin makon da a ka yi a shekarar 2018

Shalkwatar fina-finan Nollywood wadda ita ce ta uku a duniya ta na Lagos, wadda ta kunshi masu kirkira, da zane-zane, masu wasan dabe, da wasannin gargajiya, da adabi da mawaka da sauransu.

Femi Kuti ke nishadantar da 'yan kallo a wurin Afrika Shrine a LagossHakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Femi Kuti ke nishadantar da 'yan kallo a wurin Afrika Shrine a Lagos

"Lallai birnin cike ya ke da mutane masu karsashi da hazaka,'' inji Oyatogun. "Wuri ne cike da al'adu daban-daban, gidan shagulgula, da watayawa da nishandarwa, sannan yadda ake gudanar da bukukuwa a Lagos ya banbanta da na ko'ina a Najeriya, komai na mu na daban ne.''

"Akwai abubuwa masu daukar hankali a Lagos "

Daya daga cikin abin da Lagos ta yi kaurin suna akai shi ne Casu, sai kuma yadda dare baya hana gudanar da karkoki tamkar da rana. Kusan a ko da yaushe akwai casun da ake shiryawa, sannan kusan duk layin da ka bi ko unguwanni ba za ka rasa mashaya manya da kanana ba. Ga kuma gidajen casu daban-daban inda ake kwana dabdala da kade-kade ya yin da fitattun mawaka irinsu Burna Boy da Wizkid da Fela Kuti, ke kwana kayatar da mutane.

Dandazon 'yan kallo a gidan casu da ke "Afrika Shrine"Hakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Dandazon 'yan kallo a gidan casu da ke "Afrika Shrine"

Wani matashi Obuekwe ya ce "Ba bu yadda za a yi ka ji kadaici matukar ka na zuwa gidajen casu a Lagos, cibiyar nishadi ce da kayatar da jama'a kai babu yadda za ka zauna cikin kadaici sai dai idan kai ka so hakan."

Mawakin salon kidan hip-hop M.I Abaga a gidan casu a LagosHakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Mawakin salon kidan hip-hop M.I Abaga a gidan casu a Lagos

Ko da mutum ba ya ra'ayin casu da wasu raye-raye, Lagos ta tanadi wani abu na daban ga irin mutanen, duk da cewa birnin na fama da tsananin zafi, akwai tekuna daban-daban da za ka je bakin ruwa ka shakata a wasu lokutan ma iyalai kan yi kungiya dan shan iska musamman ranakun karshen mako. Akwai wuraren shakatawa da ke lambuna masu kayatarwa, da wata doguwar gada da ta ratsa cikin wani dausayi mai sassanyar iska da manyan bisshi yoyi masu korran ganyayyaki luf-luf sun yi wa lema mai ban sha'awa.

Wata mace na tafiya kan gadar da ta ratsa dajin da ke Lekki Conservation Centre a Lagos.Hakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Wata mace na tafiya kan gadar da ta ratsa dajin da ke Lekki Conservation Centre a Lagos.

"Akwai wurare na musamman da aka ware dan masu son karatu, da guje-guje, da wuraren da mutane kan je dan bayyana wata damuwa da ke damunsu a kuma ba su shawarwari, kamar yadda Emeka Okocha wani mai shirya bukukuwa ya shaidawa BBC. ya kara da cewa "Lagos wuri ne da duk abin da ka ke bukata ko nema za ka samu daidai da kai."

T

News Source:  www.bbc.com