Bom ya kashe kananan yara a Afghanistan

Bom ya kashe kananan yara a Afghanistan

Ba dai sabon abu ba ne, kananan yara su yi wasa da bom din da bai kai ga fashewa ba a Afghanistan, a sakamakon yadda aka kwashe tsawon lokaci kasar na cikin tashin hankali. 

Kimanin yara guda biyar sun rasa rayukansu a sakamakon wasu ababen fashewa da suka tarwatse a wurare biyu a birnin Herat na Afghanistan. Rahotannin da DW ta samu na cewa akwai wasu mutane 20 da ababen fashewar suka jikkata. 

HukumominTalibanmasu mulkin Afghanistan sun ce lamarin ya faru ne a ranar Jumma'a, lokacin da kananan yara suka tono ababen fashewar, suka fara wasa da su.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin d'ana bama-baman. Sai dai Taliban ta ce ta yi nasarar tono wasu karin bama-bamai guda biyu da ba su kai ga fashewa ba a kusa da in da lamarin ya faru a ranar Jumma'a.

News Source:  DW (dw.com)