EU na shirin hana 'yan Rasha shiga cikinta

EU na shirin hana 'yan Rasha shiga cikinta
Taron ministocin kasashen ketare na kungiyar Tarrayyar Turai a Jamhuriyar Czech, zai duba yiwuwar hana 'yan Rasha izinin shiga kasashen da bai wa sojojin Ukraine horo.

Shiri ne dai na musamman da aka bijiro da shi da nufin nazari kan kiraye-kirayen da ake yi na kasashen Tarayyar ta Turai su dauki mataki na bai daya da zai hana 'yan kasar Rasha takardun izinin shiga cikin su da sunan yawon shakatawa.

An dai dauki lokaci galibin kasashen Tarayyar Turan na bai wa sojojin kasar Ukraine horo kan yadda za su iya sarrafa makaman kasashen yamma da ake kai musu domin kare kansu daga hare-haren da Rasha ke kaddamarwa kan kasar tun cikin watan Fabrairu.

Yayin ma wani taro na hadin gwiwa a gefe guda, wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar tsaro ta NATO da wasu ministocin tsaron, za su tattauna kan batun dakatar da aikin kiyaye zaman lafiya da dakarun kungiyar EU da na MDD ke yi a Mali.

News Source:  DW (dw.com)