Japan ta himmatu wajen taimaka wa Afirka

Japan ta himmatu wajen taimaka wa Afirka
Kasar Japan ta yi alkawalin hada gwiwa da Afirka a yayin taron kolin Ticad a Tunis wajen karfafa tattalin arzikin wannan nahiya, domin ta samu karfin fuskantar rikice-rikice da annoba da ta'addanci da suka dabaibaye ta

 A lokacin da yake bayani a taron kolin da ya hada bangarorin biyu a birnin Tunis, firayiministan Japan Fumio Kishida ya ce lokaci ya yi da za "gyara zaluncin" da aka yi wa Afirka ta hanyar samar mata da kujera ta dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Dama dai tun da farko shugaban Senegal kuma shugaban AU Macky Sall ya tabo batun na canjin tunani, yana mai cewa dole ne kwamitin sulhu ya yi la'akari da duk abin da ke kawo rashin zaman lafiya da rashin ci gaba a Afirka. Kusan shugabannin kasashen Afirka 20 ne suka halarci taron kasa da kasa karo na takwas na Ticad da ke nazari kan gaban Afirka.

 Kasar Japan ta bayar da tallafin dala biliyan 30 ga Afirka domin horar da jami'an 'yan sanda da kula da kan iyakoki da taimaka wa shirya ingantaccen zabe a kasashen Afirka.

 

News Source:  DW (dw.com)