NATO ta yi tir da kisan fararen hula a Ukraine

NATO ta yi tir da kisan fararen hula a Ukraine

Bayan gano kisan fararen hula da dama da ake zargin dakarun Rasha da aikawa, Amirka da NATO sun nuna kaduwa da jin yadda aka yi wa fararen hula kisan kiyashi a Ukraine.

Amirka da kungiyar tsaro ta NATO sun nuna matukar damuwa game da abinda suka kira kisan kiyashi da dakarun tsaron Rasha suka yi kan fararen hula a Bucha kusa da Kiev.

A yayin da ya tattaunawa da kafar yada labarai ta CNN, babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya bayyana cewa hotunan da aka nuna na fararen hula da suka mutu a Bucha na tada hankali, kana kuma wannan wani ne daga cikin mugun ta'adin da Rasha ta ke yi a Ukraine, kana ya ambaci cewa Amirka za ta bayar da gudunmawar da ta dace don yin cikakken nazari da gabatar da batun a gaban hukumomi na kasa da kasa.

A daya bangaren babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce duniya ba za ta zura wa Rasha ido ba kawai tana ci gaba da kisan fararen hula, saboda hakan ya zama wajibi a dakatar da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.

Stoltenberg ya ce kungiyar za ta yi kokarin taimakon Ukraine ta kowane fanni musamman da makamai, wanda hakan zai kara bai wa kasar wata dama ta samun matsayi a yayin tattaunawar tsagaita buda wuta.

News Source:  DW (dw.com)