Gana ta karbi alluran riga-kafin Corona miliyan 1,2

Gana ta karbi alluran riga-kafin Corona miliyan 1,2

A Amurka, Gana ta karbi alluran riga-kafin Corona miliyan 1,2 da kamfanin Moderna ya samar don yaki da annobar.

Alluran cutar ta Covid-19 da gwamnatin Amurka ke rabawa kasashe matalauta karkashin shirin COVAX sun isa Accra babban Birnin Gana.

A karkashin shirin na COVAX a watan da ya gabata ma Gana ta karbi alluran riga-kafin Corona miliyan 1,5 wadda kamfanin AstraZeneca ya samar.

Shugaban Kasar Gana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewa, ana fuskantar samun allurar riga-kafin Corona a duniya baki daya, amma nan da watan Oktoba suna sa ran samun allurai miliyan 18.

 

News Source:   ()