Ministan Baitulmalin kasar Turkiyya ya tattauna da takwaransa na Uzbekistan

Ministan Baitulmalin kasar Turkiyya ya tattauna da takwaransa na Uzbekistan

Ministan Baitulmali da kasafin Kudin Turkiyya Lutfi Elvan ya gana da Ministan Kudin Uzbekistan Timur Ishmetov.

Elvan ya yada bayanai a kafafensa na sada zumunta game da taron inda yake cewa,

"Mun gana da Ministan Kudin Uzbekistan, Timur Ishmetov, a Tashkent. Mun gudanar da taro mai fa'ida inda muka tattauna haɗin gwiwar harkokin kuɗi tsakanin ƙasashenmu. Ina godiya ga abokin aikina mai daraja akan irin hadaka da kulawa ta kusa da nuna." 

Elvan ya kuma gana da shugaban bankin cigaban musulunci Muhammad Sulaiman Al Jasser da mataimakin firaministan Uzbekistan, ministan zuba jari da kasuwanci Sardor Umurzakov  a Tashkent.

News Source:   ()