Radamel ya bar Galatasaray

Radamel ya bar Galatasaray

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray da ke Turkiyya ta rabu da dan wasanta Radamel Falcao.

Falcao da kungiyar sun soke kwantiragin da suka kulla, inda ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar Rayo Vallecano ta Spaniya.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce, an soke yarjejeniyar da aka kulla da Falcao tare da aminewar sa.

Falcao ya saka rigar Galatasaray a kakar wasanni 2 tare da buga wasanni 43, ya jefa kwallaye 20 tare da taimakawa wajen jafa kwallaye 3.

 

News Source:   ()